Daga Edita
A wani mataki na kare lafiya da rayukan al'umma, Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu (PHIMA) da Cibiyar Yaƙi da Yaduwar Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), ta kama wani mutum da ake zargi da gudanar da haramtacciyar harkar kiwon lafiya a yankin Panshekara da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa daukar wannan mataki cikin hanzari ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu daga wasu jama'a masu kishin al'umma, dangane da wannan aiki na kiwon lafiya da ake gudanarwa ba tare da izini ba.
Ya ce, "Muna samun rahoton, nan take muka dauki mataki. Mun tura tawagar haɗin gwiwa daga Ma'aikatar Lafiya, PHIMA da KNCDC da kuma Rundunar Yan'sanda zuwa wurin, inda aka samu nasarar kama wanda ake zargin tare da masu taimaka masa. A halin yanzu ana tsare da su a Hedikwatar 'Yan Sanda ta Bompai domin ci gaba da bincike."
Dakta Yusuf ya bayyana cewa an tarar da wanda ake zargin yana raba wa mutane, wadanda aka sarin su mata ne, katin yin rijastar ganin likita da sunan wata kungiya mai zaman kanta, mai suna Brother Paul Legacy Foundation, inda yake karɓar kuɗi daga jama'a da sunan samar musu da magani.
Ya ƙara da cewa bincike da jami'an Ma'aikatar Lafiya da Hukumar PHIMA da KNCDC suka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ba ƙwararren ma'aikacin lafiya ba ne, kuma ba shi da wata shaidar cancanta da aka amince da ita a fannin kiwon lafiya.
A cewar Kwamishinan Lafiya na jihar nan, katinan rajistar da wanda ake zargin ke rabawa, waɗanda ke ɗauke da adireshi a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, suna ɗauke da alƙawarin bayar da "magani kyauta", wanda ake kyautata zaton wata dabara ce ta yaudarar jama'a domin jefa su cikin wannan haramtacciyar harka.
Dakta Yusuf ya buƙaci al'ummar jihar nan da su guji neman magani ko sauran ayyukan kiwon lafiya daga hannun masana kiwon lafiya na bogi. Ya jaddada cewa ya kamata jama'a su nemi kulawar lafiya ne kawai a cibiyoyin lafiya da gwamnati ta amince da su ko kuma daga ƙwararrun ma'aikatan lafiya.
Hakazalika, ya yabawa rundunar yan sandar jihar nan, karkashi jagorancin Kwamishina Alh. Ibrahim Bakori da jajurtattatun ma'aikatansa, sakamakon dakile wanna al'amari.
Dakta Yusuf ya kuma yabawa jama'ar da suka bayar da wannan rahoto a kan lokaci, yana mai cewa matakin nasu ya nuna muhimmiyar rawar da 'yan ƙasa ke takawa wajen kare lafiyar al'umma.
A ƙarshe, Kwamishinan ya yi kira ga jama'a da su rika kai rahoton duk wani abu da ya shafi zargin gudanar da haramtattun ayyukan kiwon lafiya ga hukumomin da suka dace ba tare da ɓata lokaci ba. Ya kuma sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Jihar Kano na kawar da masu aikin bogi a fannin lafiya, kare rayukan jama'a, da tabbatar da cewa duk ayyukan kiwon lafiya a faɗin jihar Kano ana gudanar da su bisa ƙa'ida da kuma ƙwarewa.