Thursday, September 19, 2024

KWAMITIN BIBIYA NA DMCSA YA KAI ZIYARAR GANI-DA-IDO RUMBUNAN ADANA MAGUNGUNA NA SHIYYOYI


Daga Farouk Isa Musa 

A kokarin tabbatar da wadatuwar magungunan a asibitocin jihar nan, jami'an Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar Kano sun kai ziyarar aiki zuwa rumbunan adana magunguna na shiyyar Gaya da Rano da Dambatta da kuma Gwarzo.

Darakta-Janar na hukumar ta DMCSA Famasist Gali Sule, ta bakin Jami'in Hulda da Jama'a na ma'aikatar Farouk Isa Musa, ya ce sun kai ziyarar ne don ganewa idanunuwansu yanda ayyuka suke gudana a shiyyoyin guda 4.

Famasist Gali Sule ya kara da cewa ziyarar tana da matukar muhimmanci, domin a lokacin ziyarar ne ake fahimtar nasarori da aka samu, da kuma irin kalubale da rumbunan adana magunguna na shiyyoyi ke fuskanta.

Bugu da kari, Famasist Gali Sule ya ce jami'an ma'aikatar suna kai irin wannan ziyarar gani-da-ido daga lokaci zuwa lokaci don tabbatar da komai yana tafiya kamar yanda ya kamata.

Daga nan sai ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na samar da wadatattu kuma ingantattun magunguna masu rahusa a dukkanin asibitocin da ke jihar nan.

A karshe, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar nan ya yi kira ga ma'aikatan hukumar da su kasance masu gaskiya da rikon amana a yayin gabatar da ayyukansu domin samun al'umma mai cike da koshin lafiya, wanda hakan zai samar da cigba mai dorewa.

No comments:

Post a Comment

Kano a Role Mole in Health Commodity Supply

By Farouk Isa Musa   Several states in Nigeria have been looking upon to Kano state government for guidance in terms of supply c...