Tuesday, December 31, 2024

Kwamishiniyar Ma'aikatar Yawon Bude Ido Ta Kai Ziyarar Gani da Ido Zuwa Hukukomi Guda Biyu

Daga Amina Lawan Isah 

Kwamishiniyar Hajiya Aisha Lawan Saji Rano wanda ta gudanar da Ziyarar ta tane a yau 30 ga watan Disamba na shekarar 2024 ta kai wa Hukumar Adana Tarihi da Al'adu da Kuma Hukumar Yawon Bude Ido ziyarar ta bayu ne domin duba yanayin yanda suke gudanar da ayyukansu da kuma ganin yadda za a ciyar da hukumomin gaba
  
  A Lokacin da ake Gudanar da Ziyarar kwamishiniyar Hajiya Aisha Lawan Saji ta Yaba da Kokarin da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake a wannan Hukumomin dake Karkashin Ma'aikatar Yawon Bude Ido da Al'adu Don ganin An Bunkasa Al'adu Ta Kara da cewa ta ga duka Hukumomin An gyara ginunsu sun dawo sababbi 
   
  Saji ta Yaba da irin Kokarin da suke na ganin sun ciyar da Hukumomin Gaba da kirkiro sababbin Abubuwan Al'ada da dawo da na da, da aka manta Domin ciyar da ma aikatar Gaba
 
  Kwamishiniyar ta Yi Kira Ga daukacin Ma'aikatan Hukumomin Yawon Bude Ido da Raya Al'adu da su Guji Fashi na aiki da kin zuwa aiki da wuri tace saboda ba hujja akan Haka Domin Mai Girma Injiniya Abba Kabir Yusuf shine Gwamnan da ya fara biyan Karin Albashin A watan da yai Alkhairi 

  A nasu Jawabin Babban sakatare Na Hukumar Adana Tarihi da Al'adu Ahmad Abba Yusuf da Kuma Takwaransa Babban Darakta na Hukumar Yawon Bude Ido Kwamrad Tukur Bala Sagagi sun tabbar da Hadin Kai da Goyan baya Ga kwamishiniya ta yadda za'a Kai ga nasara

No comments:

Post a Comment

Kano DMCSA Receives Business Excellence Award

By Farouk Isa Musa   The Kano State Drugs and Medical Consumables Supply Agency (DMCSA) has recorded another milestone as the ag...