Tuesday, January 14, 2025

Majalisar Dokoki Ta Jihar Kano Za Ta Hada Hannu Da DMCSA Don Inganta Sashin Lafiya


Daga Farouk Isa Musa 

A wani ho66asa na mussaman don ha6aka harkar kiwon lafiya, Majalisar Dokoki Ta Jihar Kano ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tallafawa Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar nan don ganin ta sauke nauyin da aka dora mata.

Mambobin Kwamitin Lafiya na Majalisa ne suka bayyana haka a lokacin da suka ka6i bakuncin shugabannin Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar Kano (DMCSA), karkashin jagorancin Darakta-Janar na hukumar, Famasist Gali Sule, wadanda suke je harabar majalisar don yiwa 'yan Kwamitin bayani a kan ayyukan ma'aikatar da kuma tarin nasarori da ta samu a shekara daya da rabi.

Da yake jawabi a lokacin ganawar, Mataimakin Kakakin Majalisar, Honoabil Muhammad Bello Butu-butu ya tabbatar wa da shugabannin Hukumar ta DMCSA cikakken goyon bayan Majalisar domin inganta samar da magunguna a fadin jihar nan.

Daga nan sai Mataimakin Kakakin Majalisar ya yabawa irin namijin kokari na shugabanni da ma ma'aikatan Hukumar Samar da Magunguna ta Jiha.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Lafiya na Majalisar Dokoki Ta Jihar nan, Honorabil Zakariyya Alasan Ishaq, wanda kuma shi ne dan majalisa mai wakiltar Kura da Garun Mala, ya jinjinawa Famasist Gali Sule sakamakon tarin nasarori da ya samu a cikin gajeren lokaci.

A tasa gudunmawar, dan majalisa mai wakiltar maza6ar Ungogo a zauren majalisar, Honoabil Aminu Sa'ad ya yi kira da sauran hukumomi a jihar nan da su yi koyi da Hukumar Samar da Magunguna ta hanyar zage damtse domin ciyar da jihar nan gaba.

Da yake jawabi tun da fari, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano, Famasist Gali Sule ya ce sun je Zauren Majalisar ne don sanar da 'yan Kwamitin irin aikace-aikacen hukumarsa da nasarori da hukumar ta samu da kuma kalubale da take fuskanta.

Famasist Gali Sule ya kara da cewa kadan daga cikin irin nasarorin da hukumar ta samu sun hada da biyan sama da kaso 60 na bashin da ake bin wannan hukuma wanda aka gada daga gwamnatin da ta gabata, da kuma samar da ingantattun magunguna masu rahusa daga kaso 30 zuwa kaso 96.

Haka kuma, yawan asibitocin da Hukumar take bai wa magunguna sun karu daga guda 814 zuwa 890. Haka zalika, Hukumar tana gudanar da taron masu ruwa da tsaki duk bayan watanni uku don tabbatar da ana yin komai bisa tsari kuma a bude, in ji shi.

No comments:

Post a Comment

Kano HMB Set to Distribute N55M Worth Hydroxyurea, Thousands CS, Delivery Packs

By Aisha Tahir Saraki  As part of its continued monthly intervention, Kano State Hospital Management Board is set to distribute ...