Sunday, April 27, 2025

Kwamitin Tuntuba na NNPP Ya Bayar Da Gudunmawar Kudi Ga Iyalan Wadanda Suka Rasu a Gombe


Daga Maryam Abubakar Tukur

'Yan Kwamitin Tuntu6a a Za6en Shugaban Kasa na Jam'iyyar NNPP a Jihar Gombe, karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Famasist Gali Sule, sun kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon wani hadarin mota da ya faru a garin Billiri da ke Jihar Gombe.

Da yake jajanta wa iyalan mamatan, Famasist Gali Sule Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano, ya bayyana hadarin a matsayin abun takaici.

Daga nan sai ya mika gudunmawar kudi Naira 200,000 ga iyalan marigayan a madadin 'yan Kwamitin.

Haka zalika, Darakta-Janar din ya yi addu'ar samun sauki ga wadanda suka ji raunuka a sakamakon ibtila'in.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin da ta gabata ne, 21 ga watan Afrilu, wata  babbar mota daukar kaya ta murkushe wasu mabiyar addinin Krista a garin Billiri da ke jihar Gombe a lokacin da suke tattaki a wani 6angare na bikin Easter. A sakamakon haka, mutane biyar suka rasu, yayin mutane 13 kuma suka ji munanan raunuka.

Yayin wannan ziyara, mambobin Kwamitin sun sami rakiyar jagororin jam'iyyar NNPP na jihar Gombe karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar na riko Dakta Abdullahi Mohammed Wali.

Kadan daga cikin 'yan Kwamitin da suka kai wannan ziyara sun hada da Sakataren Zartarwa na Hukumar Karen Hakkin Mai Saye da Mai Sayarwa ta Jihar Kano Alh. Zangina Jafaru, Shugaban Matasa na Riko na Jam'iyyar NNPP na jihar kano Alh. Auwalu Kibiya, Hajiya A'in Jafaru Fagge, Abubakar Usman Kibiya da kuma Alh. Mukhtar Tijjani Kura.

No comments:

Post a Comment

FRSC vows to enforce safety rules, regulations in Kano

By Bosede Olufunmi The Federal Road Safety Corps (FRSC) has vowed to enforce safety rules and regulations on road users, especia...