Daga Wakilinmu
Kungiyar Pharmacy Gali Sule/Abba Gida-Gida Support Group ta sha alwashin yin aiki ba dare ba rana domin ganin jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zabukan kasa na shekarar 2027.
Darakta Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano (DMCSA), Pharmacist Gali Sule, ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci shugabannin kungiyar don kai wa Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Karamar Hukumar Nassarawa, Hon. Hassan Hussain, ziyara a ofishinsa.
Da yake jawabi, Pharmacist Gali Sule, wanda shi ne uba kuma jagoran kungiyar, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin karfafa alaka da kuma tattauna hanyoyin da za a bi wajen yin aiki tare, domin tabbatar da hadin kai da nasarar jam’iyyar APC da daukacin ‘yan takararta a zaben 2027.
Ya ce wannan ya hada da kokarin ganin jam’iyyar ta samu nasara tun daga matakin Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Alhaji Kashim Shetima, zuwa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Hon. Murtala Sule Garo, da ‘yan majalisun dattawa, wakilai da na jiha baki daya.
Da yake nasa jawabin, Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Karamar Hukumar Nassarawa, Hon. Hassan Hussain, ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan ziyara, yana mai yabawa Pharm. Gali Sule da shugabannin kungiyar bisa wannan muhimmiyar girmamawa da suka nuna masa.
Hon. Hassan Hussain ya kuma jinjina wa Pharmacist Gali Sule bisa dimbin nasarorin da ya samu a Hukumar DMCSA cikin shekaru uku da suka gabata. Ya bayyana cewa irin jajircewa da sadaukarwar da Pharmacist Gali Sule ke nunawa wajen gudanar da ayyukansa abin a yaba ne, yana mai cewa da irin wannan jajircewa ta yawaita a tsakanin masu rike da madafun iko, da an samu ci gaba mai yawa fiye da wanda aka samu a halin yanzu.
Ya tabbatar wa shugabannin kungiyar da cikakken goyon baya da hadin kai wajen kokarin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC daga sama har kasa a zaben shekarar 2027.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Kungiyar Pharmacy Gali Sule/Abba Gida-Gida Support Group, Alhaji Iliyasu Idris Dantiye, ya bayyana aniyar kungiyar ta yin aiki kafada-da-kafada da sauran kungiyoyin magoya baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a Jihar Kano da kasa baki daya.
Alhaji Dantiye ya bayyana cewa kungiyar tana da mambobi daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano, wadanda suka hada da jajirtattun matasa maza da mata, da kuma gogaggun ma’aikata da suka yi ritaya. Ya kara da cewa kungiyar tana da rajista da jam’iyyar APC.
Daga karshe, Shugaban kungiyar ya gode wa Hon. Hassan Hussain bisa kyakkyawar tarbar da ya yi wa shugabannin kungiyar, tare da yaba masa bisa goyon baya da hadin kan da yake bai wa kungiyar.
No comments:
Post a Comment