Tuesday, December 24, 2024

DMCSA Za ta Hada Hannu da NDLEA don Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi

Daga Farouk Isa Musa 

Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano DMCSA ta nemi hadin kan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA reshen Jihar Kano don yakar mummunar ta'adar nan ta ta'ammaali da miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin ma'aikatan gwamnati.

Shugaban Hukumar Samar da Magunguna ta Jiha, Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar aiki zuwa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi da ke nan Kano a safiyar Litinin din nan.

Famasist Gali Sule ya nuna damuwarsa sakamakon yanda shan miyagun kwayoyi ya zama ruwan dare, musamman a tsakanin matasa, a fadin jihar nan.

Shugaban ya ce za su yi wa dukkanin ma'aikatan hukumar, ciki har da shugannin ma'aikatar, gwajin shan miyagun domin tabbatar da da'a.

Haka zalika, hukumar za ta shirya taron wayar da kai a kan illar shan miyagun kwayoyi, in ji shi.

Da yake jawabi, Kwamandan hukumar ta NDLEA reshen jihar Kano Abubakar Idris Ahmad, wanda ya sami wakilcin Mukaddashin Kwamanda Yaya Muhammad Aminu, ya ce ma'aikatarsa a shirye take domin hada kai da Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar Kano domin yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Daga nan sai ya yabawa Famasist Gali Sule bisa wannan hagen nesa.

No comments:

Post a Comment

Kano DMCSA Receives Business Excellence Award

By Farouk Isa Musa   The Kano State Drugs and Medical Consumables Supply Agency (DMCSA) has recorded another milestone as the ag...