Daga Maryam Garba Balarabe
A wani yunkuri na inganta harkar kiwon lafiya a fadin jihar nan, jami'an Hukumar Kula da Asusun Kiwon Lafiya na Jihar Kano (KHETFUND) sun kai ziyarar aiki zuwa Makarantar Koyar da Aikin Unguwarzoma da ke garin Dambatta, a ranar Laraba 22 ga watan Oktoba 2025, domitn tantance yanda aka kashe kudade da Hukumar ta bai wa makarantar don daukar nauyin dalibai masu rubuta jarabawar kammala karatu.
A ranar 10 ga watan Oktoba na shekarar 2025, Hukumar KHETFUND ta samar da kudi Naira miliyan daya da dubu dari takwas da saba'in da takwas (N1,878,000) don biyan kudin jarrabawar karshe ga daliban Makarantar Koyon Aikin Unguwarzoma ta Dambatta.
Da take jawabi a kan makasudin ziyarar, Shugabar Hukumar KHETFUND Dakta Fatima Usman Zahraddeen ta ce sun je makarantar ne don bibiya da tantancewa ayyuka don tabbatar da cewa an kashe kudaden da hukumar ta samar bisa doka da oda.
Dakta Fatima Usman Zahraddeen, wacce ta sami wakilcin Daraktan Tsare-Tsare Aminu Usman Giwa, ta jadadda aniyar hukumar na bibiyar yanda aka yi tasarufi da kudaden da ta samar domin tabbatar da an yi amfani da su kamar yanda aka tsara.
Daga nan sai Shugaban Hukumar KHETFUND ta godewa Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa bijiro da managartan tsare-tsaren kiwon lafiya a fadin jihar nan.
Haka zalika, ta yabawa Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf bisa hadin kai da goyon baya da yake bai wa hukumar ta KHETFUND.
A lokacin ziyarar, jami'an na KHETFUND sun duba dakin kwanan daliba a makarantar domin gyara shi, wanda shigabanin makarantar suka mika bukatar gyaran nasa, don samar da jin dadi da walwala ga dalibai.
A nata jawabin, Shugabar Makarantar Koyon Aikin Unguwarzoma ta Dambatta, Kaltume A. Maikano ta jinjinawa KHETFUND bisa irin ayyuka da take gudanarwa a makarantun kiwon lafiya da asibitoci da ma ma'aikatun gwamnati a lungu da sako na jihar nan.
No comments:
Post a Comment